Ephesians 5

1Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun ‘ya’yansa. 2Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah.

3Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi. 4Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya.

5Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah. 6Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun ‘ya’ya. 7Kada ku yi tarayya tare da su.

8Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar ‘ya’yan haske. 9Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya. 10Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi. 11Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su. 12Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su.

13Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su. 14Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, “Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka”.

15Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima. 16Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne. 17Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji.

18Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki. 19Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji. 20Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba. 21Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu.

22Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji. 23Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki. 24Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu.

25Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta, 26Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma. 27Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi.

28Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa. 29Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya. 30Domin mu gabobin jikinsa ne.

31“Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya”. 32Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa. Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.

33

Copyright information for HauULB